16 Satumba 2026 - 22:17
Source: ABNA24
Hamas: Rugujewar Ginin Al-Sa'adah Wani Sabon Babi Ne Na Yaƙin Kisan Kare Dangi A Gaza

Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a yau (Laraba) ta ɗorawa gwamnatin Sahayoniya alhakin rugujewar ginin Al-Sa'adah a kan mazauna da 'yan gudun hijira a birnin Gaza kuma ta kwatanta wannan lamari a matsayin sabon babi na musiba ga ɗan adam mai ban tsoro na yaƙin kisan kare dangi kan Zirin Gaza. Tun da sanyin safiyar yau, ƙungiyoyin agaji na Falasɗinawa sun ciro gawar shahidai 20 ciki har da yara 6 daga ƙarƙashin baraguzai kuma wasu da dama har yanzu ba a same su ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a yau (Laraba) ta ɗorawa gwamnatin Sahayoniya alhakin rugujewar ginin Al-Sa'adah a kan mazauna da 'yan gudun hijira a birnin Gaza da mutuwar wasu mutane kuma ta kwatanta wannan lamari a matsayin sabon babi na matsanancin yanayin wahalar ɗan adam mai ban tsoro na yaƙin kisan kare dangi kan Zirin Gaza.

Hamas a cikin sanarwarta ta bayyana: wannan bala'i ci gaba ne kai tsaye na yaƙin kisan kare dangi a Zirin Gaza kuma ta yi nuni da cewa laifuffukan maƙiya ba su takaita ga jefa bama-bamai kan fararen hula, lalata gidajensu da kai kisan kiyashi a kansu ba.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa: sakamakon yaƙin a yau yana ci gaba da rugujewar gine-ginen da suka lalace kuma da ke gab da faɗuwa; gine-ginen da 'yan ƙasa suka fake a ciki, a yanayin da aka yi mummunar barna ga gidaje da unguwannin zama.

Hamas ta yi gargaɗi cewa ƙarancin injunan cire baraguzai da tarkace da kayan agaji, yana barazanar cewa yayin da sa'o'i masu muhimmanci ke wucewa, rayukan mutane da yawa za su iya salwanta.

Ƙungiyar ta yi kira ga gaggawar yunkurin ƙasa da ƙasa don shigar da manyan injuna da kayan ceto da kare fararen hula don ƙungiyoyi su iya isa ga waɗanda suka makale.

Hamas ta yi gargaɗi game da babban bala'in ɗan adam; a yanayin da jami’an kare fararen hula suka ba da labarin kasancewar gine-gine kusan 2,000 da ke gab da faɗuwa, na zama da kuma barazana waɗanda ke jefa rayukan dubban 'yan ƙasa cikin haɗari na gaske da ke ci gaba.

Hamas ta nanata cewa jagorancin wannan ƙungiyar a cikin tarurruka da tuntuɓe da suka gabata da masu shiga tsakani da ɓangarorin ƙasa da ƙasa, sun nemi gaggauta yunkuri da motsawa don dakatar da bala'in ɗan adam da mamayar ke haifarwa wanda sakamakonsa ke ci gaba a Zirin Gaza.

Ƙungiyar ta bukaci masu shiga tsakani, gwamnatin Amurka da cibiyoyin ƙasa da ƙasa masu alaƙa da su ɗauki nauyin da ya rataya a wuyansu kuma nan take su ɗauki mataki don kawar da ƙuntatawa da ke hana shigar da kayan ceto da injunan da ake buƙata da shawo kan wannan haɗari da samar da yanayin zama mai aminci ga 'yan ƙasar da yaƙi da lalacewar gidajensu suka ja su zuwa zama a cikin gine-ginen da suka lalace kuma da ke gab da faɗuwa.

Ƙungiyoyin kare fararen hula ta Falasɗinawa tun da sanyin safiyar yau sun ciro gawar shahidai 20 ciki har da yara 6 kuma wasu da dama har yanzu suna ƙarƙashin tarkacen ginin zama na "Al-Sa'adah" wanda ya ruguje a tsakar dare a yankin Al-Sina'ah a yammacin birnin Gaza.

................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha